×
Home: Mobile Home: Original Style Christian Netflix Jewish Stories X-Witch X-Muslim MP3 Bible Bible Movies Gospel Videos Godly Movies CBN Videos Kids Videos Worship Music Vids for New Believers Random Video What's New
  Kat Kerr   Anna Rountree   Mary Baxter   Several #1   Several #2   Choo Thomas   Ian McCormack   Burpo   I saw His Glory   7 Colombian Youths   Heavenly Blood   Heaven Testimonies
  Lazarus   Bill Wiese   Mary Baxter   Dr. Rawlings   J. Perez   Hepzibah   Ptr. Park   7 Columbian Youths
  Atomic Prayer   Prayers that ROUT demons   Warfare + Blessing   Healing   Declaration   101 Decrees   Tongues   Rosary   Artic Fire   Why Should We Pray?   Why Bother
  MP3 Bible   10 Commandments   Learn Bible in 24 Hours   40 Spiritual Lessons   Alpha   Foundations   Bible Commentaries   Book of Mormon   Temple Study   Red Letters   Divine Healing Training   God Story   Gap Theory   Creation to Christ   Book of John   Kids Bible Cartoons   Derek Prince Teaching   Jesus Film   Digital Bible   Bible Codes ELS
  Passion of Christ   New Jesus Film   Introduction   Names of God   Jesus IS...   Jesus Film   That's My KING   Father's Love Letter   Celestial Hug
  Warfare Training 1   Warfare Training 2   Casting Out demons   Combat   Examples   Warrior King   Exorcism   Prayer   Ask Him   demonology   Clarita   NUWI
  Final Quest   The Call   Tommy Hicks   3 Days   Angel Song   The Prison   H.A.Baker
  Best #1   Best #2   Spiritual Food   Generals   Ramirez   Bishop Kelley   Gary Wood   Roland Buck   Rees Howells   Baptized by Fire   Sid Roth   Todd White   Gary Beaton   Victor Marx   Akiane   Theo Nez   Nun's Story   Retha McPherson   Tomas Welch
  Booth's Vision   Frank Jenner   Hell's Best Kept Secret   EE-Taow   Manifesting Power   LivingWaters   Atheist Delusion   Using AI for Jesus   Sharing w/ Muslims   Sword + Serpent
  Revival Hymn   Jesus in China   Freemason Curruption   Modern Child Sacrifice   the WAR on Children   XGay   Transformations   Ark of Covenant   Soul Ties   Last Reformation   Noah's Ark Found   Does GOD Exist   Political Issues   Fake Mountain   7 Mountains   ID vs Evolution   Bible Science   American History   China Records   Case: Creator   Case: Christ   Case: Faith   Little Lessons   Deadly Mistakes   Enemies Within   Chinese Characters   Global Warming   The Final Frontier   Understanding Israel   Testing Joseph Smith   Targeting Kids
  X-Muslim   Journey of Hope   Islam Rising   ACT   Jihad   Best Muslim Story   Enemies Within   Answering Islam   Killing for Heaven   Killing the Infidel
  Downloadable MP3 Worship Music   Online Worship Music  DivineRevelations University   Free Posters   Christian Pictures   Kids Christian Cartoons   Bible Trivia   End Times Visions   Fractal Praise   Communion Verses   Bobby Conner   Brother Yun   Civil War   Prayer Tank   Fiscal Cliff   Understanding Economics   Who takes the Son   Christian GPTs
  All Languages   Afrikaans   Albanian   Amharic   Arabic   Bengali   Bulgarian   Burmese   Cambodian   Catalan   Chinese   Czech   Danish   Dutch   Farsi   Finnish   French   German   Greek   Gujarati   Hausa   Heberw   Hindi   Hungarian   Indonesian   Italian   Japan   Kannada   Khazanah   Korean   Laos   Malagasy   Malayalam   Malaysian   Marathi   Mongolian   Nepali   Norwegian   Oriya   Polish   Portuguese   Punjabi   Romanian   Russian   Somali   Samoan   Serbo_Croatian   Sinhala   Slovak   Slovenian   Spanish   Swahili   Swedish   Tagalog   Tamil   Telugu   Thai   Tongan   Turkish   Ukrainian   Urdu   Uzbek   Vietnamese
 About  Disclaimer  Phone# USA 425-610-9216  [email protected]
Follow on YOUTUBE  YouTube Follow on Facebook  Facebook Follow on X/Twitter  X/Twitter Follow Podcast RSS  Podcast  RSS Follow on Instagram  Instagram Follow on TikTok  TikTok
  PDF Library   Believer's Authority   Heavenly Man, Yun   Torch + Sword   The Harvest   Faith Shoemaker's Vision   Daughter of Sacrifice
AI Tech Site Something Funny... 2nd Page, Older Material
×






Menu / Home
Menu / Home

HTML Bible Gospel Go The Prophet's Story Passion of the Christ The Jesus Film 4 Spiritual Laws
Ruya Game Da Aljanna     WAHAYI AKAN JAHANNAMA     Muslim Dreams/Mohammed  MP4 Hi Low      LOKACI NA WUCEWA DA SAURI

….(Shaida na daya)….

(Luka 16:19)

Akwai wani mai-arziki wanda yana sanye da shunaiya da  farare masu-kawa, yana annishuwa kowache rana, yana zari: da wani maroki, sunansa Li’azaru, wanda aka ajiye a bakin kofarsa, chike da gyambuna, yana marmari a chiyadda shi daga gutsatsarin da ke faduwa daga tebir na mai-arzikin nan; I, har karnuka su kan zo su lasa gyambunansa. Ananan marokin ya mutu, mala’iku suka dauke shi suka kai shi chikin kirgin Ibrahim: mai-arzikin kuma ya mutu, aka yi masa kushewa. A cikin Hades ya tada idanunsa sama, yana cikin azaba ya ga Ibrahim daga nesa, da Li’azaru a cikin kirjinsa. Ya tada murya ya ce, Abba Ibrahim, ka yi mani jinkai, ka aiko Li’azaru shi tsoma kan yatsansa cikin ruwa, shi sanyaya harshe na; gama azaba ni ke ji cikin wannan wuta.

Amma Ibrahim ya ce, Dana, ka tuna, kai cikin kwanakin da kana da rai kana samun naka kyakkyawan abu, Li’azaru kuma hakanan nasa masifa: yanzu daganan ana yi masa ta’aziya, kai kuwa kana shan azaba. Banda ko wannan duka, tsakanin mu da ku akwai babban rami a kafe domin wadanda su ke so su tashi daga nan su haye zuwa wurin ku kada su sami iko: kuma domin kada kowa shi ketaro daga chan zuwa wurinmu.

Littafi Mai Tsarki, maganar Allah ya bamu bayani mai haske game da sama da jahannama. A wannan wajen da muka karanta, Ubangiji yayi mana maganar wurare guda biyu: sama da kuma jahannama, yanke hukunci ko ceto. Babu tsaka-tsaka, babu kuwa wani wurin da wadanda suka yi laifi za su je a wanke su domin su iya shiga sama. Babu ‘kasa tana dabo’ inda mutane za su zauna na lokaci kadan idan sun bar duniya kamin su je sama. Littafi Mai Tsarki ya ba mu bayani mai haske game da wannan.

(11 Afirilu 1995)

Allah ya ba mu wahayin nan domin ya canza yanayin rayuwar mu. Mun fara sanin wanene Allah da maganarsa kenan. Mu matasa ne guda bakwai wadda Allah ya bayyana kansa gare mu, ya kuma ba mu hakin gayawa duniya wannan wahayin.

Duk wadannan abubuwan su fara faruwa ne a misalin karfe goma (10) na safe. Muna addu’a kuma muna da shirin zuwa wurin shakatawa daga baya. Ba zato ba tsammani, kamar karfe goma, sai muka ga wata haske mai karfi ta haskaka daga taga. Da wannan hasken ta bayyana sai dukkan mu muka fara magana a cikin harsuna, an yi mana babtizma da Ruhu Mai Tsarki.

A  lokacin, dukan mu munyi mamaki da kuma sha’awar abinda muka gani. Wannan hasken na haskaka dukan dakin. Hasken ta fi hasken rana. A tsakiyar wannan hasken kuwa mun ga mala’iku masu yawa sanye da fararen kaya. Mala’ikun nan kyawawa ne, dogaye, abin son gani.

A tsakanin mala’ikun nan kuma mun ga abin mamaki – siffar mutum.Wannan siffar na sanye da fararen tufafi. Gashin sa kamar zaren zinariya. Ba mu iya ganin fuskarsa ba domin hasken na da tsanani. Amma, mun ga bel a kirjinsa wadda na zinari ne, a jinkin bel din an rubuta “Sarkin Sarakuna, Ubangiji Iyayengiji”. Takalman sawayensa na zinari ne, babu kamanin kyaunsa. Da muka ga wannan mutumin, dukan mu, muka sunkuya da gwiwarmu.

Sai muka fara jin muryarsa. Muryarsa na da dadi, kuma abin alajibi; kowanne kalma da ya fadi na sukar zuciyar mu kamar takobi mai kaifi biyu; kamar yadda aka rubuta a maganar Allah (Ibraniyawa 4:12). Ya yi magana a cikin murya sassauka amma mai iko. Mun ji shi ya ce “ ‘Ya’yana kanana, kada ku ji tsoro, ni ne Yesu banazare, na ziyarce ku ne domin in nuna maku abin mamaki don ku fadi ku kuma nuna wa garuruwa, kasashe, birnaye, majami’u da dukan wurare. Inda na ce ku je, can za ku je, inda na ce kada ku je, baza ku je ba”.

Littafi Mai Tsarki, Maganar Allah ya ce a Joel 2:28: “Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama’a duka, ‘ya’yanku mata da maza za su iyar da sakona, tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, samarinku za su ga wahayi da yawa”. Wannan ne lokacin da Allah yake shirya wa kowa.

Sai wani abin mamaki ya faru, wata dutse ta fito a tsakiyar dakin. Ubangiji kuma da ke nan da mu Ya sa mu hau kan dutsen. Girman dutsen kamar inchi takwas ne daga kasa, kuma, wata babbar rami ta bayyana a kasan dakin. Ramin babbace, baki da kuma  ban tsoro. Nan da nan muka fadi daga saman dutsen zuwa cikin ramin da ke kasar dakin. Ramin na da duhu kuma ya kai mu ga tsakiyar duniya.

Da muke cikin dukukun duhun nan, mun tsorata sosai! Mun ji tsoro har muka ce wa Ubangiji “Ubangiji ba mu so mu je wannan wajen! Kada ka kai mu can Ubangiji! Ka dauke mu daga nan ya Ubangiji!” Ubangiji Ya amsa da kyakkyawar murya cike da tausauyi ya ce “Ina so ku ga wadannan abubuwan domin ku gaya wa wasu”

Mu na cikin wata rami mai kamar kaho, sai mun ga innuwa,  aljannu da siffofi suna yawo. Mun cigaba da sauka kasa. A cikin dakika kadan, mun ji gun ya zama kamar fanko da kuma gagarumar tsoro.

Sai muka isa wasu koko, masu kofofi mai ban tsoro da hanyoyi da zaka iya batawa. Ba mu so mu shiga ba. Mun ji wari da zafin da ya shake mu. Da muka shiga mun ga siffofi masu ban tsoro. Duk wajen na cike da harsunan wuta, a tsakiyar wutan akwai mutane dubai da suke shan azaba. Abin ban tsoro ne har ba mu so mu kalli abin da ake nuna mana ba.

An raba wurin zuwa sashi daban-daban na azaba da wahala. Sashi na farko da Ubangiji ya yarda mana mu gani shi ne wadda muka kira “kwarin kasko”. Akwai miliyoyin kaskuna wadda aka saka su a kasa, dukan su kuwa suna tafasa da aman wutar dutse. A cikin kowannensu, ran mutumi ne wanda ya mutu kuma ya je jahannama.

Da wadannan rayukan su ka ga Ubangiji, sai suka fara ihu da kururuwa suna cewa “Ubangiji ka yi mana jinkai! Ubangiji, ka ba ni daman barin wannan wajen! Ubangiji, ka fitar da ni, ni kuwa zan gaya wa duk duniya wannan wurin gaskiya ne!” Amma Ubangiji bai kalle su ba, akwai miliyoyin maza, mata da matasa a wannan wurin. Mun ga ‘yan luwadi da mashaya suna ta shan azaba. Mun gan su duk suna ta ihu domin babbar azaban da suke sha.

Mun firgita, yadda muka ga jikinsu na hallaka. Tsutsotsi suna ta shiga da fita daga ramin idon su, da bakin su, da kunnuwan su; suna kuma shiga ta cikin fatarsu a koina a jikinsu. Wannan cikar Maganar Allah ne wadda aka rubuta a Ishaya 66:24 “Sa’ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taba mutuwa ba, wutar da take kona su kuma ba za ta taba mutuwa ba. Dukan mutane za su ji kyamarsu”.  Haka nan ma a Markus 9:44 “A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta”. Mun razana da abin da muke gani. Mun ga harshen wuta  masu tsawon kafa 9 zuwa 12. A cikin kowanne harshen wuta akwai ran wanin da ya mutu ya je jahannama.

John LennonUbangiji ya yardar mana mu ga daya daga cikin mutanen da suke kaskon nan. Mutumin na kife, duk tsokar fuskar sa tana fadiwa. Yana kallon Ubangiji da duk niyarsa; sai ya fara ihu yana kiran sunan Yesu, yana cewa “Ubangiji ka yi mani jinkai, Ubangiji ka ba ni wani zarafi Ubangiji ka dauke ni daga nan!” Amma Ubangiji Yesu bai so ya kalle shi ba. Yesu ya juya masa baya. Da Yesu ya yi haka, sai mutumin ya fara zagi, yana sabo ga Ubangiji. Wannan mutumin sunansa John Lennon ne, dan kungiyar kidan na shaidan da ake kiran su “The Beatles”. John Lennon mutum ne wadda ya yi ba’a da kuma was da sunan Ubangiji a lokacin da yake da rai. Ya na cewa wata rana adinin Krista zai bace, kowa kuma zai manta da Yesu. Amma a yau, mutumin nan na jahannama, Yesu Kristi kuma ya na da rai! Adinin Krista kuma bai bace ba.

Sai muka fara tafiya a bakin wannan wajen, rayukan  da ke gun kuma suna mika hannayen su garemu suna rokon jinkai. Suna ta rokon Yesu ya cire su daga wannan wurin, amma Ubangiji bai ko kalle su ba.

Sai muka fara shiga yanki daban-daban na wannan wajen. Sai muka isa yankin jahannama, inda azaba ya fi tsanani; tsakiyar jahannama. Azabar na gun babu dan Adam da zai iya furtawa. Mutanen da suke nan, mutane ne wadanda sun san Yesu da Maganar Allah. Su fastoci, masu bishara da duk wadda sun taba karban Yesu, sun kuma san gaskiya amma sunyi rayuwa iri biyu.

Akwai wadanda sun ja da baya daga bin Yesu; wahalarsu ya fina sauran so dubu. Suna ta ihu, suna rokon Ubangiji ya  yi masu jinkai amma maganar Ubangiji ya ce a Ibraniyawa 10: 26-27 “In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na’am da sanin gaskiya, to ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubi, sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi wadda za ta cinye makiyan Allah.”

Wadannan rayukan suna wurin domin sun yi wa’azi, sun yi azumi, sun yi wakoki, sun kuma daga hannayen su a majami’u amma a layi da kuma gidajen su, su masu zina ne, masu faskanci, da karya da fashi. Ba za mu iya yin karya wa Allah ba. Littafi Mai Tsarki ta ce “duk wanda aka ba abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gareshi” (Luka 12:48)

Sai Allah ya yarda mana mu ga wasu mata biyu da su ‘yan’uwa ne a cikin Kristi lokacin da su ke duniya, amma, ba su yi rayuwar tsarki ba a gaban Ubangiji. Daya ta fadi wa dayan “ke la’antaciyar talaka! Laifin ki ne ya sa ina nan! Ba ki yi mi ni wa’azin bishara mai tsarki ba! Ba ki kuma gaya mi ni gaskiya ba, yanzu ina jahannama!”

Za su fada wadannan abubuwan wa junan su a tsakiyar wuta, sun kuma tsani junansu domin babukauna, ko jinkai, ko yafewa a jahannama.

Akwai duban rayuka da sun san Maganar Allah amma rayuwarsu ba ta da tsabta a gaban Ubangiji mai tsarki. “Ba za ka yi wasa da Allah ba ko da harshen wutan jahannama!” in ji Ubangiji. Ya kuma ce mana “’Ya’ya na, duk wahalolin duniya, idan an tara a waje daya ba kome ba ne, BA KOME BA NE idan an kwatanta shi da wahalar da mutum za ya ji a jahannama”. Idan wahalar yana da tsanani ga wanda ba ya sha wahala sosai ba a jahannama, yaya za a gwada tsananin wahalar wadanda ke tsakiyar, wadanda suka san Maganar Ubangiji amma suka juya masa baya. Ubangiji Ya ce mana, za mu iya wasa da wutar da ke duniya amma ba wutar jahannama.

Mun cigaba da tafiya zuwa wurare daban-daban, Ubangiji kuma ya nuna mana mutane daban-daban. Mun ga mutanen da azabar su a kalla iri shida ne. Akwai wasu kuma da aljannu suke ba su azaba iri daban-daban. Wani irin hukunci kuma shi ne na zuciyar su, mai cewa “ka tuna lokacin da ake yi maka wa’azi, ka tuna da lokacin da ka ji maganar Allah, ka tuna lokacin da aka yi maka magana game da jahannama ka yi dariya!” Zuciyar su tana ta ba su azaba; kamar yadda tsutsotsi da su ke tafiya a duk jikin su, kamar yadda wuta da ke cin su ya fi wutan da muka sani sau dubu-dubai. Wannan shi ne ladar da ibilis ya keda shi domin duk wanda ya bi shi.

Maganar Allah ya ce a Ruya ta Yohanna 21:8 “Amma matsorata, da marasa amana, da masu aikin kyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk makaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai wuta da kibritu, wanda yake shine mutuwa ta biyu.”

Daga bisani, Ubangiji  ya nuna mana wani mutum wanda ya kashe mutune shida. Wadannan mutane shidan na nan kewaye da shi, suna yi masa ihu suna cewa “laifin ka ne ya kawo mu nan, LAIFIN KA NE!” Mai kisan kan ya rufe kunnuwansa domin baya so ya saurare su, amma ba zai iya gudun sauraronsu ba domin a jahannama duk hankali da tunanin mutum zai dawo.

Rayukan da ke wannan wajen suna shan azaban kishin ruwa da ba za a iya jimrewa ba kuma wanda ba za su taba gamsuwa ba; kamar labarin Liazaru da mai arziki. (Luka 16:19) Mai arzikin a wutan jahannama yana son digo daya na ruwa, da zai ishe shi. Maganar Ubangiji ya ce a Ishaya 34:9 “Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, kasar za ta zama kibirtu, wato farar wuta. Dukan kasar za ta kone kamar kalo.”

Fruit Tree of fireA wanchan wajen, kowane rai na tsakiyar wuta. Mutanen sukan ga kawalneniyar ruwa a tsakiyar wuta amma idan sun yi kokari su kaisu, sai ruwar ta zama wuta. Sukan ga itatuwa wanda ‘ya’yan su ke bada ruwa amma idan sun yi kokarin cire ‘ya’yan, sai ya kona hannunsu, aljannun kuma saisu yi ta musu ba’a.

Sai Allah ya kai mu wajen da ya fi sauran wuraren da muka gani tsanani. Mun ga tafkin wuta, a gefe daya na tafkin akwai wata karamar tafki. A wannan karamar tafkin akwai rayuka miliyan, miliyan da suke ta kuka su na rokon Ubangiji ya yi masu jinkai. Suna ce masa “Ubangiji ka taimake mu, ka dauke mu daga nan! Ka taimaka, ka ba mu dammar fita!!!” Amma Ubangiji ba zai iya yi masu komi ba domin an shirya shari’ar su.

A tsakanin wannan miliyoyin mutanen, Ubangiji ya yardar mana mu kura idon mu a kan wani mutum wadda rabin jikinsa na cikin wuta. Ubangiji ya ba mu fahimta da kuma sanin tunaninsa. Sunan mutumin nan Mark ne. muna mamakin abubuwan da mutumin nan ya ke ce wa kansa a tunanin sa. Mun koyi dawwamammen  darasi da muka ji wannan tunanin nasa “zan bada koda menene domin in zama a wurin da ku ke yanzu! Zan ba da koda menene domin in koma duniya ko da na minti daya ne. Ba zan damu ba in ni ne mafi rashin jin dadi,ko mafi ciwo, ko wadda aka fi tsana, ko  mafi talauci a duniya duka, zan bada ko da me ne don in koma duniya na minti daya.” Ubangiji Yesu na rike da hannuna. Yesu ya amsa wa tunanin Mark ya ce “Mark, me ya sa ka ke so ka koma duniya ko da na minti daya?” Da muryar kuka da wahala, ya ce wa Yesu “Ubangiji! Zan ba da koda menene domin in koma duniya na minti daya domin in tuba, in sami ceto.”

Da Ubangiji  ya ji abinda Mark ya fadi, sai na ga jini ya fito daga ciwon Yesu, hawaye kuma sun cika a idanunsa da ya ce “Mark,ya yi maka latti! An shirya tsutsotsi domin gadon ka, tsutsotsi kuma za su rufe ka.”(Ishaya14:11). Sa’an da Ubangiji ya fadi wannan masa, sai ya fada a cikin tafkin har abada. Abin bakin ciki shi ne, duk wadannan rayukan ba su da bege kuma. Mu da mu ke duniya ne muke da zarafin tuba yau domin mu je sama tare da Ubangiji Yesu Kristi.

Na bar ku da ‘yar uwata ta cigaba da wannan shaida, na gode.

 

….(Shaida na biyu, Lupe)….

Allah ya yi maku albarka ‘yan’uwa kaunatattu. Bari mu karanata Maganar Ubangiji daga Zabura 18:9 “Ya bude sararin sama ya sauko kasa, tare da girgije mai duhu a karkashin kafafunsa”

Sa’anda Ubangiji ya mika mani hannunsa, na kama hannun sai muka fara sauka kasa cikin wannan rami. Ramin yana ta kara duhu har ga lokacin da ba na ganin dayan hannuna,wadda ba shi ne ke rike da hannun Ubangiji ba.

Kwaram sai muka wuce wani abu mai duhu da kuma kyalkyali; wadda kuma na da hayaniya. Wajen na da duhu sosai da hannunka ma baza su iya samun bangon ramin ba. Saukar mu na da sauri sosai har na ji kamar raina na fita daga jikina.

HellSai na ji wari kamar na rubabben abu, kamar rubabben nama. Warin yana ta karuwa a kowanne lokaci. Sai na ji muryar miliyoyin rayuka. Suna ihu, suna kuka, suna makoki mara karewa. Na tsorata sosai sai na juya wajen Ubangiji na ce “Ubangiji ina ka ke kai ni? Ubangiji ka yi mani jinkai! Ka yi mani jinkai!” Ubangiji ya ce “Tilas ne ki ga wannan domin ki iya gaya wa kowa.”

Mun cigaba sauka cikin rami mai kamar kahon nan, har mu ka isa wani wurin da gabaki daya duhu ne. Kamar an cire mani labule a ido, sai na ga miliyoyin harsunan wuta. Na ji radadin kururuwa amma ban ga kowa ba. Na tsorata kwarai. Saina ce wa Ubangiji:“oh, Ubangiji, ka yi mani jinkai! ka yi mani jinkai! kada ka kai ni wannan wajen! Ka yafe ni!” A wannan lokacin ban yi tunani wai ni ‘yar kallo ba ne, na aza ranar shari’a ne. Jiki na, na rawa sosai domin na dauka karshen rayuwa na ne kenan.

Mun gusa kusa da wata harshen wutan da ke gaban mu; harshen babba ce kuma tana ci da fushi. Na cigaba da sauka da hankali, ina ta ganin harsunan wuta dayawa, ina ta jin miliyoyin rayuka suna kuka da murya daya.

Table with bottlesSai na ga tebur na katako, wadda ba ya konewa. Akwai kwalabe kamar na giya a kan sa. Kwallaben kamar na shakatawa ne, amma suna cike da wuta. Da ni ke kallo sai wani mutum ya bullo. Namar jikinsa ya kusan gama rugurguzaiwa, abin da ya rage daga tufafinsa kuma a cike da laka kuma suna konewa. Idanunsa da bakinsa da duk gashin sa sun kone a cikin wutan. Yana iya gani na koda shike bai ya da ido. Ina gaya ma ku cewa ran mutum ne ke tunani, shi ne kuma ya ke gani da gaskiya ba gangan jikin mutum ba.

Mutumin ya mika ramammen hannunsa wajen Ubangiji, yana kuka, yana cewa “Ubangiji ka yi mani jinkai! Ubangiji ka yi mani jinkai! Ina cikin azaba! Ina konewa! Ka yi mani jinkai, ka dauke ni daga wannan wajen!” Ubangiji ya dube shi da tausayi, sai na fara jin abu mai dumi a hunnuna. Na duba na ga, jini… jinin Yesu! Jinin Ubangiji ya fito a hannunsa da ya ke kallon mutumin nan mai shan azaba, a rufe da wuta.

Sai mutumin ya juya ya dubi teburin, ya kuma fara tafiya ta gun. Ya dauki kwalba daya amma da zai sha daga ciki sai wuta da hayaki sun fito daga cikin kwalbar. Ya mai da kansa baya, ya yi kururuwa kamar wanda ban taba ji ba. Ya yi kuka mai zafi da kuma bakin ciki, sai ya fara shan abin da ke cikin kwalbar. Ashe kwalbar na cike da ruwar batir ne, kuma sai ya rugurguzar da makokoronsa gabaki daya. Zaka iya ganin ruwan batir din na shiga cikin sa yana yi masa rauni.

An kwarzana lambar 666 a goshin mutumin nan. A kirjin sa akwai wata faranti da aka yi da wasu irin karfe da ba za a iya hallakawa ba, ko da da wuta ne ku tsutsotsi. Ya na da harufai da aka rubuta wadda bamu gane ba. Ubangiji a cikin jinkansa ya ba mu ma’anar abin da aka rubuta. “Ina nan domin ni mashayi ne” Ya roki Ubangiji ya yi masa jinkai amma Maganar Allah  yayi magana dalla-dalla a cikin I Korantiyawa 6:10 “Ko barayi, ko makwadaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gado a cikin mulkin Allah.”

Ubangiji ya nuna mani rayuwar mutumin na karshe a duniya kamar fim. Kamar babban talabijan ne ya ke nuna mani dakikan sa na karshe kafin ya mutu. Wannan mutumin sunansa Luis ne, yana shan giya a mashaya, na ga wannan tebirin da wadannan kwalaben a mashayan. A zagaye da tebir din abokanensa ne. (Zan iya gaya maku wannan yanzu, ABOKI DAYA NE NA GASKIYA, sunan sa YESU KRISTI. Aboki ne na kwarai). Luis na shan giya, abokanansa ma sun rugada sun bugu. Babban abokinsa ya fasa kwalba sai ya fara sukansa. Da ya ga Luis a kwance a kasa sai ya gudu, amma Luis ya zub da jini har ya mutu a kasa a wajen. Abin bakin ciki shi ne ya mutu ba tare da Ubangiji ba.

A tsakiyar  duk wannan, da duk rayukan jahannama suna ta kuka, sai na tambaye Ubangiji:“ya Ubangiji, ka gaya mani, wannan mutumin ya san batun ka? Ya san batun ceton ka ne?” Ubangiji ya amsa da bakin ciki ya ce:“I Lupe, ya san da n. ya karbe ni in zama mai cetonsa amma bai bauta mi ni ba.” Sai na kara jin tsoro. Luis ya kara kuka da karfi yana kuma  ihu, “Ubangiji wannan na da zafi! Wannan na da zafi! Ka yi mani jinkai!” ya sake mika hannunsa ga Ubangiji, amma Yesu ya rike hannuna muka tafi daga wancan harshen wutan. Sai wutar da ke cin Luis suka dadda rikicewa, kuma ya kara  karfin kukansa, “Ubangiji ka yi mani jinkai! Ka yi mani jinkai!!” Sai ya bace a cikin wutan.

Mun cigaba tafiya, wannan wajen kato ne kuma da ban tsoro! Mun kusanci wata harshen wuta kuma sai na ce wa “Ubangiji, a’a! Ba na so in ga wannan abu kuma! Ina rokonka, ka gafarta mani! Ka gafarta mani! Ba na son in ga wannan!” Sai na rufe idanu na, amma bai hana kome ba don ko idanu na a bude ko rufe, ina ganin kome. Harshen wutan ya fara sauka kadan-kadan, sai na ga wata mata jikin ta duk laka wanda akwai tsutsotsi a ciki. Suman kan ta kuma kadan ne kawai ya rage, laka kuma ya yi funkaso a jikinta. Tsutsotsin na cinyeta, ta ko ina, ta na ihu “Ubangiji ka yi ma ni jinkai! Ubangiji ka yi ma ni jinkai ka yafe ni! Ka dube ni! Wannan abu na yi mani rauni! Ka yi ma ni jinkai! ka dauke wannan tsutsotsin! Ka dauke ni daga wannan azaba domin ya yi mani rauni sosai!” Ubangiji ya dube ta ne kawai da bakin ciki. Da mu ka rike hannunsa mun ji zafi da bakin cikin da ya ke zuciyar Shi domin duk rayukan da suka bata, masu konewa har abada a cikin wutan jahannama.

Wannan matan ba ta da ido ko lebe amma tana gani tana kuma ji; zafin sai karuwa ya ke yi. Ta na da kwalba a hannun ta cike da ruwan batir wadda ta dauka wai turare ne. Ina ganin cewa ruwan batir ne, kuma duk lokacin da ta fesa a jikinta, ya na kunan ta. Ta na ta cewa, turare ne mai tsada. Ta yarda cewa tana sake da abin wuya mai kyau, amma ni na ga macizai ne kewaye da wuyar ta. Ta kuma yarda cewa ta na sake da abin hannu mai tsada amma na ga tsutsotsi wadanda sun kai tsawon kafa daya suna tona cikin kasusuwanta. Ta ce kayan adonta su ne duk abin da ta ke da shi, amma na ga kunama da tsutsotsi a duk jikin ta. Ta na da faranti na karfe da kowa a jahannama ke sake da shi. An rubuta a kai, “Ina nan ne don fashi.”

Wannan macen ba ta da-na-sani domin zunubinta. Ubangiji Ya tambaye ta: “Magdalena, me ya sa ki ke wannan wajen?” Ta amsa ta ce “Bai dame ni ba in yi sata daga wurin wasu. Abu daya tak kawai ne ya dame ni, in sami kayan adona, kuma in sami turare masu tsada. Ban damu ba ko na yi fashi, idan dai zan yi kyau”

Na rike hannun Kristi da na ga tsutsotsin su na tona jikin ta. Magdalena ta juya tana neman wani abu. Sai na sake tambayan Ubangiji: “Ubangiji wannan macen ta ji labarin Ka?” Ubangiji Ya amsa Ya ce: “I, macen nan ta sanni.”

Magdalena ta fara kalle-kalle tana cewa, “Ubangiji ina macen da ta kan yi mini maganar Ka? Ina ta ke? Ina nan a jahannama shekaru goma sha biyar (15) ke nan.” Dukan mutanen da ke jahannama suna iya tuna kome. Magdalena ta yi ta tambaya “Ina macen? Ban gan ta ba!” Na san jikin taba zai iya juyawa ba domin namar jikin ta na waje daya. Ta yi kokari ta juya ta kalli wasu harsunan wuta, ta nemi macen da ta yi mata magana game da Allah. Ubangiji Ya amsa mata Ya ce “A’a! A’a, Magdalena bata nan.Wannan macen da ta gaya  mi ki game da Ni tana tare da Ni a mulkin sama.”

Da jin haka, sai ta wurga kanta a cikin wuta wanda ya kone ta sosai. Farantin karfen ya yanka mata hukuncin sata. Ina so ku karanta Maganar Allah a Ishaya 3:24 “Maimakon su rika kanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin damara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanko, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!”

Da muka cigaba da tafiya da Ubangiji, na ga wata babbar ginshiki cike da tsutsotsi. A kewaye da shi akwai wajen zamewa na karfe ja don zafi. A kan ginshikin nan akwai  allon-talla mai haske wanda za a iya gani daga ko ina. A kan allon-tallan an rubuta “Maraba duk makaryata da magulmata.” A karshen wajen zamewar akwai karamar ruwa da ke tafasa. Ya yi kama da dutsen da ke ci da wuta. Sai na ga mutum tsirara ya na saukowa daga wajen zamewar. Idan suna zamewa sai fatar jikin su ta bare, ta mannu a da abinda ke kawo zamewar. Sa’an da sun fada cikin ruwa mai tafasan sai harshen su ya kumbura har ya fashe sai tsutsotsi su fito a maimakon harshen. Wannan shi ne farkon azaban su. Maganar Allah ya ce a Zabura 73:18-19 “Hakika ka sa su a wurare masu santsi, ka sa su fadi su hallaka sarai! Cikin kyaftawar ido aka hallaka su, suka yi mummunan karshe!”

Bayan ganin wannan, an komar da mu jahannama. Ina so in gaya muku cewa sama da jahannama gaskiya ne, fiye da duniyan nan da muka sani. A nan ne za ka zaba wacce hanya ne ka ke so ka bi; ka yi rayuwa har abada da Yesu ko kuma a cikin wutar jahannama. Ubangiji yana ta ce mana “Ku kuma zama a tsarkake in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji, Ku kuma zama a tsarkake in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.” (Ibraniyawa 12:14) Shi ya sa na ke kara fadi yanzu cewa “babu wanda zai ga Ubangiji in bai yi zaman tsarki ba”

 

…. (Shaida na uku, Sandra)….

Bari mu duba Mganar Ubangiji a Littafin Matta 10:28Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kuruwarsa sai dai ku ji tsoron wannan da ke da ikon hallaka kuruwar da jikin duka a gidan wuta.”

Duk sa’anda  wani rai ya iso jahannama, wannan mutum yakan mallaki jikin mutuwa. Ubangiji Yesu Ya rike hannu na, sai mu ka fara tafiya  kasa ta cikin wata rami mai duhu da kuma zurfi da ya  shiga tsakiyar duniya. Mun isa wani wuri mai kofofi dayawa; daya daga cikin ya budu sai mu ka shiga tare da Ubangiji. Na ki in bar hannun Ubangiji domin na sani idan na sake zan zauna har abada a jahannama.

People hung up on wallsDa muka shiga kofar, na ga wata katuwar bango. Akwai duban mutane da an rataya da kai da kugiya hannayen su kuma a daure da mari a jikin bangon. Mun kuma ga duban mutane suna tsaye a tsakiyar harsunan wuta.

Mun je gaban daya daga cikin harshen wutan sai wutan ya fara sauka da hankali. Sai na ga wani mutum a ciki, da ya yi magana na gane na miji ne. Mutumin na sake da kayan fada mai kazanta da kuma a fattatake. Tsutsotsi su na ta yin sululu ciki da wajen jikin mutumin. Ya na nan kamar an kona shi da wuta. An cire idanunsa, fatarsa kuma suna narkewa su fadi a kasa. Amma bayan fatan sun fadi, za su sake girma a jikin shi sai kuma kome ya fara daga fari.

Da mutumin nan ya ga Yesu ya ce “Ubangiji Ka yi mani jinkai! Ka taimake ni, ka dauke ni daga nan na dan lokaci! Na minti daya!” a kirjin wannan mutumin akwai farantin karfe wanda an rubuta, “ina nan ne don fashi.” 

Sa’anda Yesu Ya matso kusa, Ya tambaye shi “Menene sunanka?” Mutumin ya amsa ya ce “Andrew, suna na Andrew, Ubangiji”. Ubangiji ya tambaye shi “Tun yaushe ka ke nan?” Andrew ya amsa ya ce “Na dade a nan.” Mutumin ya fara bada labarinsa. Ya ce yana da nauyin karban zakka da shirya raba kudi ga talakawan majami’an Katholika. Amma sai ya sata kudin.  Da ido cike da tausayi, Ubangiji ya tambayi mutumin “Andrew, ka taba jin bisharan ceto?” Andrew ya amsa “I Ubangiji, akwai wata mace krista da ta je majami’a ta yi wa’azi bisharan ceto sau daya amma ban so in karba  ba. Ban  so in gaskanta ba amma yanzu na gaskanta! Yanzu na gaskanta gaskiya ne! Ina rokon ka Ubangiji ka dauke ni daga nan ko da na lokaci kadan ne!”

Da ya ke magana tsutsotsi na yawo a ramin idonsa, su na fita ta kunen sa suna shiga kuma ta bakinsa. Ya yi kokari ya cire su da hannunsa amma ya gagara. Yana ta ihu mai tsanani, yana rokon jinkai a wurin  Ubangiji. Yana ta rokon Yesu ya dauke shi daga wannan wurin. Akwai kuma aljannu wadanda su keta masa azaba, suna sukan sa da mashi. Aljannun sunyi kama da yar-tsana  da ke duniya da ake kira “Jordanos”. Na ga wannan yar-tsanan a jahannama amma ba yar-tsanan ba ne kuma, suna da rai, suna kuma yin shaidanci. Suna kamar kafa uku a tsawo, suna da kuma hakora masu kaifi, jini na fitowa daga bakin su, idanun su kuma jajaye.

Suna sukar Andrew da dukan karfin su da kuma sauran mutanen da suke wannan bangaren jahannaman. Da na ga haka, na tambayi Ubangiji yaya za a yi yar-tsana a duniya ta yi kama da aljanni. Ubangiji ya ce mani wadancan ruhun bakin ciki ne.

Da muka cigaba, mun ga mutane dubai a cikin azaba. Duk lokacin da wani rai ya ga Ubangiji, sai su mika ramammen hanayen su. Na kulla da wata mace da ta fara ihu da ta ga Yesu. Ta yi kururuwa “Ubangiji ka yi mani jinkai! Ka dauke ni daga nan!” ta na wahala sosai, ta mika masa hannu, tana rokon sa ya fitar da ita daga wannan wurin ko da na dakika daya ne. Ta na nan tsirara, laka ya rufe jikin ta. Ta yi kokari ta cire su da hannun ta amma duk sa’anda  ta cire su sai su karu sosai. Tsutsotsin  suna da tsayin inchi shida zuwa takwas (6-8). Maganar Allah ya ce a Markus 9:44 “A wurin tsutsotsi masu masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.”

Abu mai tsanani ne ganin macen nan da kuma jin kukan ta yayinda tsutsotsin su ke chin naman jikin ta. Akwai farantin karfe da ke kirjinta wanda wuta ba ya hallaka shi. An rubuta “ina nan ne saboda zina”. Kamar  yadda zunubinta ya ke, an sa matan nan dole ta yi zina a jahannama da wani kibaben, kazamin maciji. Macijin na da kato-katon kayoyi a jikin shi ma su tsawon inchi shida zuwa takwas. Wannan macijin ya shiga cikin gindin ta, ya yi yawo a cikin jikin ta har zuwa makokoronta. Da macijin ya shige ta sai ta fara kururuwa.

Macen nan ta roki Ubangiji Ya dauke ta daga wannan wurin, “Ubangiji, ina nan saboda zina, na yi shekaru bakwai, tun lokacin da na mutu da wannan cuta mai katya garkuwar jiki (AIDS). Ina da masoya guda shida, ina nan saboda zina.” A jahannama dole ta rika yin wannan zunubi akai-akai. Ba ta da hutu dare da rana ta na wannan wahala. Ta yi kokarin mika hannun ta ga Ubangiji amma Ubangiji Ya ce ma ta “Blanca, kin yi lati, tsutsotsi za su zama gadon ki, za su kuma rufe ki” (Ishaya 14:11) Da Ubangiji ya fadi wadannan kalmomin, wata bargon wuta ya rufe ta, ban iya ganin ta ba kuma.

Lake of FireMun cigaba da tafiya, mu na ganin duban mutane. Akwai matasa, manya da dattawa su na shan azaba. Mun isa wani wuri mai kama da babban wajen yin iyo na wuta, da duban mutane maza da mata a ciki. Kowannen su suna da farantin karfe a kirjin su wanda aka rubuta “ina nan saboda ba na ba da zakka da kuma baiko.” Da na karanta wannan sai na tambayi Ubangiji “Ubangiji, yaya haka zai faru, cewa mutanen nan suna nan saboda wannan dalilin?” Ubangiji ya amsa ya ce “I, domin wannan mutanen sun dauka cewa zakka da baiko ba su da muhimmanci, bayan magana na ya nuna cewa doka ne.” Malakai 3:8-9 ya ce “Mutum zai iya zambatar Allah? Amma ku kuna zambatata kuna kuwa cewa, ‘Ta kaka muka zambace ka?’ A wajen al’amarin zakka da hadayu, kuke zambatata. Dukanku la’antattu ne gama al’ummar duka zamba take yi mini!”

Ubangiji Ya ce mani cewa idan mutanen sa sun rike zakkar su, yana hana aikin Ubangiji, ba za a yi bishara ba. Mutanen da ke nan suna shan wahala so dubu fiye da sauran, domin sun san maganar Ubangiji amma sun yi rashin biyayya.

Da muka cigaba da tafiya Ubangiji ya nuna mani wani mutum, ina gani daga kunkumin sa zuwa kansa, sai na fara ganin wahayin yadda ya mutu. Sunan sa Rogelio ne, yana cikin motarsa lokacin da wani ya matso kusa yayi masa wa’azin bishara, ya kuma ba shi Littafi mai Tsarki. Amma Rogelio ya ki galgadin wannan mutumin, ya cigaba a hanyar sa, bai sani cewa bayan wasu mintoci motarsa zata fadi. Ya fadi cikin wata magudan ruwa sai ya mutu.

A lokacin da ya fadi, Littafi Mai Tsarki ya budu zuwa Ruya ta Yahaya 21:8 “Amma matsorata, da marasa amana, da masu aikin kyama, da masu kisankai, da fasikanci, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk makaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibirtu, wanda yake shine mutuwa ta biyu”

Ya yi wata daya ne a wurin, yana da sauran nama a fuskarsa, kodashike yana shan wahala kamar kowa. A farko dai bai san dalilin da yake jahannama ba, amma ina zaton cewa lokacin da kristan nan ya kusance motarsa, shi ne zarafin sa na karshe ya karbi Yesu. Hakanan dayawa sun sami zarafin karban Yesu. Yau, ina gayyatan ka ka bude zuciyar ka ga Yesu; shi ne kadai hanya, shi ne gaskiya, shi ne rai. (Yohanna 14:6) Ta wurinsa ne kadai za mu sami ceto zuwa mulkin sama (Ayukan Manzani 4:12) Ubangiji ya kuma gaya mana mu bi hanyarsa da tsarki da kuma daraja.

Allah ya albarkace ku.

 

....(Shaida ta hudu)....

Yan’uwa, Allah ya yi maku albarka. Da Ubangiji ya rike hannuna na ga ina tsaye a kan dutse, a bayan mu kuma na ga mala’ika. Sai mu ka fara sauka cikin wata rami da gudu. Da na juya sai na ga mala’ikan ya tafi, sai na ji tsoro. Na tambayi Ubangiji “Ubangiji I na mala’ikan? Me ya sa bai ya nan kuma?” Ubangiji Ya ce mani “Ba zai iya zuwa wajen da za mu je ba.”

Mun cigaba da sauka kasa, sai chan mu ka tsaya karaf daya kamar a lif. Na ga wasu ramumuka, sai muka bi ta wurin da ‘yar uwata Sandra ta yi magana akai. Ramin inda mutanen ke rataye ta kawunansu da kugiya da kuma mari’a hannayen su. Bangon da ke rike da mutanen na da tsawo sosai, duban mutane kuma na rataye a kai. Su na da tsutsotsi a jikin su. Da na kalli chan gaba sai na ga wani bango kamar wannan. Sai na ce wa Ubangiji “Ubangiji! Akwai mutane dayawa a nan!” Nan da nan wata aya ta shiga zuciya ta; wani da ban sani ba. Ubangiji Ya ce mani “Muradin mutum kamar lahira ya ke, a kullum ba ya koshi” (Misalai 27:20)

Cauldron of fireMun bar wajen, sai muka isa wani waje mai suna “kwarin kasko”. Wannan kasko na cike da laka mai tafasa, sai muka matsa kusa da wurin. Mutum na farko da na gani wata mace ce. Jikin ta na iyo ya kuma nutse a cikin lakan nan mai tafasa, amma da Ubangiji Ya dube ta, ta daina motsi, sai ta tsaya a cikin lakar daga kunkumin ta. Ubangiji Ya tambaye ta “Menene sunan ki?” Ta amsa da cewa “suna na Rubiella ne.”

Sumar ta na cike da tafasasen lakan nan, namanta na rataye a jikin kasusuwan ta wanda sunyi baki domin wuta. Tsutsotsi suna shiga ta ramin idanunta, suna fita ta bakinta. Suna shiga kuma ta hanjinta suna fita ta kunnuwanta. Inda tutsotsi ba za su iya shiga ba saisu yi rami domin su sami shiga, wannan kuma na sa ciwo mai zafi.

Ta yi ihu:“Ubangiji ina rokon Ka! Ka dauke ni daga wannan wajen. Ka yi mani jinkai! ba zan iya cigaba haka ba kuma! Ka sa ya daina ya Ubangiji! Ba zan iya jimrewa ba! Ka yi mani jinkai!” Ubangiji Ya tambaye ta dalilin da ta ke nan. Ta ce ta na nan saboda girman kai, wadda shi ne aka rubuta a farantin karfe da ke kirjin ta. A hannunta akwai wata ‘yar kwalba, amma a gare ta turare ne mai tsada. Rubeilla takan dauki kwalban nan wanda a cike ne da ruwan batir, ta fesa duk jikin ta. Wannan ya kan sa duk fatar da ta fesa ya narke, wannan yana sa mata zafi sosai.

Ta yi ihu ga Ubangiji: “Ubangiji ka yi mani jinkai! Ba zan iya zama kuma a nan ba! Ubangiji dakika daya.” Ba wai ina cewa amfani da turare zunubi ba ne amma Ubangiji Ya gaya mana cewa wannan macen na wajen ne saboda turaren ta, kamar yadda maganar Ubangiji ya ce mana a Kubawar Sharia 5:7 “Kada ka kasance da wadansu gumaka sai ni.” Ta na wurin ne saboda kyau, turare da girman kai sune farko a rayuwarta. Duk da haka Ubangiji Yesu sarkin sarakuna ne, Ubangiji Iyayengiji ne kuma, dole ne Ya zama na farko a rayuwar ka; shi ya sa take wannan wurin. Da bakin ciki Ubangiji ya dube ta ya ce “Rubeilla, ya yi latti, tsutsotsi za su zama gadon ki, tsutsosi kuwa za su rue ki.” Da Ubangiji Ya fada wannan sai bargon wuta ya rufe ta. Yayin  da jikinta na cinyewa a cikin kasko, ta sha azaba mai tsanani.

Sai muka bar wannan wurin da nesa muka kuma isa wani wuri mai katon kofofi. Da muka kusance su sai kofofin suka budu mana. A dayan gefen mun ga katon kogon duste. Da na kalli sama sai na ga hasken wuta masu launi daban-daban suna matsawa kamar girgijen hayaki. Nan da nan sai na ji kida; salsa, ballenato, rock da sauran sanannun kida da wakokin da mutane ke ji a radiyo. Ubangiji Ya yi motsi da hannunsa sai mun ga mutane milliyan-milliyan a rataye da sarka a hannayen su suna tsalle a wuta.

Ubangiji Ya dube mu ya ce: “Ku duba, wannan shi ne sakamakon masu rawa.” Sukan yi tsalle sosai, sama da kasa suna bin karan kidan. Idan kidan salsa, ne sai su yi tsalle bisa ga kidin, in kidan ya canza, sai tsallen su ya canza zuwa kidan. Ba za su taba iya daina tsallen ba. Amma abu mafi tsanani shi ne a karkashin takalmansu akwai abubuwa masu tsinin inchi shida. Duk sa’anda sun yi tsalle sai su soki kafafun su, kuma basu da hutu ko kadan. Idan wani yayi kokari ya tsaya, sai shaidanu su zo nan da nan su soke shi da mashi, su zage su, suna cewa “Ku daukaka shi! Wannan dokar ku ne yanzu, ku daukaka shaidan, ku daukaka shi! Ba za ku daina ba, ku daukaka shi! Ku daukaka shi! Dole ku daukaka shi! Dole ku yi tsalle! Dole ku yi rawa! Ba za ku daina ba ko na dakika daya!”

Abin bakin ciki ne ganin cewa yawancin mutanen Krista ne, wadanda su san Ubangiji amma suna kulab na dare a lokacin da suka mutu. Wata kila ka na tambaya, “Ina aka fadi a Littafi Mai Tsarki cewa rawa haram ne?” A Yakubu 4:4 maganar Allah ya ce “Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gaba ce da Allah ba? Saboda  haka, duk mai son abuta da duniya ya maida kansa mai gaba da Allah ke nan.” Haka kuma a 1Yahaya 2:15-17 “Kada ku kaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa yake kaunar duniya, ba ya kaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. Duniyar kuwa tana shudewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” Ka tuna fa duniya za ta shude, za ta hallaka amma wanda ya bi nufin Allah zai tsaya har abada.

Dan’uwana da kuma abokina, da muka bar wannan wajen, mun ga wani abu kamar gada da ya raba lahira zuwa sashe daban-daban na azaba. Mun ga wani ruhu yana tafiya a gada na kafa. Ya na kama da doli da muka gani a duniya; muna kiran su Treasure Trolls. Launin sumar su daban ne, suna da tsofofin fuska amma da jikin yara; ba su da jikin saduwa na mjiji da mace. Idanun su na cike da mugunta. Ubangiji Ya yi mana bayani cewa, wadannan ruhohi ne na hasara. Wannan da muka gani yana rike da mashi, ya na tafiya da fadin rai a kan gadan nan, kamar shi mai sarauta ne.

Yana tafiya yana sukan mutanen da su ke kasa da mashin sa. Sai ya zage su ya ce “ku tuna da ranar da kuke wajen majami’a kuma ba ku shiga ba? Ku tuna da ranar da aka yi maku wa’azi kuma ba kun ki ji? Ku tuna da ranar da aka ba ku’yar takardar bishara amma ku ka wurgar?” Rayukan da sun bata sai su  yi ta rufe wurin da kunuwansu da suke. Sai su amsa cewa “Ka yi shuru! Ka yi shuru! Kada ka kara gaya mani! Ba na son in sani! Ka yi shuru!” Amma, ruhun nan yana jin dadin abin da yake yi domin ciwon da yake sa a ran su.

Mun cigaba tafiya da Ubangiji. Da muka ga mutane dayawa, mun lura daya daga cikin su yana ihu fiye da sauran da suke konewa a wajen. Ya na cewa “Uba, Uba, ka yi mani jinkai!” Dama Ubangiji ba zai tsaya Ya kalli mutumin ba amma da Ya ji kalmomi “Uba” Ya juya. Yesu  ya dube shi sai Ya ce “Uba? Ka kira ni Uba? A’a, Ni ba Ubanka ba ne kuma kai ba dana ba ne. idan kai dana ne, da ka na tare da ni a mulkin sama. Kai dan ubanka shaidan ne.” Nan da nan sai bargon wuta ya taso ya rufe jikin sa.

BurningUbangiji Ya gaya mana labarin wannan mutum. Mutumin ya kira shi Uba domin ya san shi. Mutumin yakan je majami’a, ya saurare Allah ta wurin Maganar sa, kuma ya karbi alkawalan Allah dayawa. Sai muka tambaya “Me ya faru Ubangiji? Me ya sa ya ke nan?” Ubangiji Ya amsa “Ya na rayuwa iri biyu; yana wata rayuwa a gida, wata kuma a ikilisiya. A zuciyarsa yana cewa ‘babu wanda ya ke kusa da ni, babu fasto ko wani dan’uwa, saboda haka zan yi duk abin da na ga dama’. Amma ya manta cewa idannun Ubangiji na kan duk abubuwan da muke yi, babu kuma wanda zai yi karya ko ya boye wa Ubangiji.”

Maganar Ubangiji ya gaya mana cewa “Kada fa a yaudare ku, ai ba a iya zambatar Allah. Duk abinda mutum ya shuka, shi zai girba.”  (Galatiyawa 6:7)  Wannan mutum yana wahala sau dubu fiye da sauran, yana biyan hukunci biyu: daya na zunubansa, daya kuma na tunaninsa cewa zai iya rudin Ubangiji.

A yau, mutane suna kokari su kasa zunuban su bisa ga girman su; suna tsammani yan luwadi, da barayi, da masu kisan kai, zunuban su ya fin a masu karya da gulma. Amma a idanun Ubangiji, dukan zunuban nan suna da nauyi daya, hukuncin su ma daya ne. Littafi Mai Tsarki ya fadi cewa “Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawami cikin Almasihu Yesu Ubangijimu.” (Romawa 6:23)  (Ezekiyel18:20) Abokai na da yan’uwa na, ina gaiyatanku, ku karbi gaiyatan Yesu. Yesu yana mika hannun jinkan sa gare ka in ka tuba. Maganar Allah ya gaya mana cewa idan mutum ya canza hanyoyinsa, ya tuba, za a yi masa jinkai. ya fi kyau ka gaskanta yanzu akan ka jira ka sha wahala daga baya. Allah ya albarkace ku.

 

....(shaida ta biyar)....

 Maganar Allah ya ce a (Romawa 6:23) “Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawami cikin Almasihu Yesu Ubangijimu.”

Da muka je chan kasa, na ji zafi na kuma dandana yadda mutuwa take. Na tsorata da abinda na gani. Na gane cewa mutane dayawa sosai a wurin; duk suna ihu da kuma kuka. Wajen bakin duhu ne, amma tare da Ubangiji duhun ya bace. Mun ga duban rayuka suna kuka domin taimako da jinkai. Suna kuka ga Ubangiji ya dauke su daga wannan wurin. Mun kuma  ji zafi sosai domin mun san yadda Ubangiji ya ke bakin cikin duk sa’anda ya gansu.

Da yawa su kan yi kuka ga Ubangiji ya fitar da su ko dana minti daya ne. Ubangiji sai ya tambaye su, “Me ya sa ku ke so ku fita?”, sai su amsa, “Domin ina son ceto! Ina so in tuba, in sami ceto!” Amma yayi masu latti.

Mutanen da suke sauraro na yanzu, yanzu ne kadai zarafin da muke da shi mu zaba wajen zaman mu na har abada. Ko ka zabi wajen ceto na har abada, ko kuma wajen hukunci na har abada.

Mun kara shiga ciki, na ga kasan da muke tafiya a kai yana hallaka da wuta; laka da harshen wuta suna ta fitowa. Akwai kuma wari mai karfi ko ta ina. Hankalin mu sun tashi, wari da ihun mutanen nan sun dame mu kwarai.

Soul trapped in burning mudSai mu ka ga wani mutum a nesa, wadda daga kunkumin sa yana nitse a cikin laka mai konewa. Duk sa’anda ya fitar da hannunsa, sai naman ya fita daga kashin, su fadi cikin lakan. Muna ganin wani abu kaman hazo a cikin kasusuwan sa, sai mu ka tambayi Ubangiji ko menene. Wannan irin hazon na cikin kowa da ke jahannama. Ubangiji Ya ce mana kuruwar rayukansu ne aka kama cikin jikin zunubi, kamar yadda aka rubuta a Wahayin Yahaya 14:11 “Hayakin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, wadannan masu yi wa dabar nan siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”

Mun fara fahimtar abubuwa dayawa da mun kyale a duniya; mafi muhimmanci shi ne cewa yadda muka yi  rayuwa a duniya shine zai nuna inda zamu yi rayuwa har abada.

Da muke tafiya hannu da hannu da Ubangiji, mun gane cewa jahannama yana da bangarori dabam-dabam kuma dayawa na azaba. Mun je wani wuri mai dakin kurkuku dayawa dauke da rayuka masu shan azaba. Aljani kala-kala ne masu ba su azaba, suna cewa “ku la’anannu, ku daukaka shaidan! Ku bauta masa kamar yadda kuka yi a duniya!” Tsutsotsin nan na ba wa rayukan nan wahala sosai; wutan kuma kamar ruwan batir ne a duk jikin su.

Mun ga wasu mutane biyu a cikin dakin kurkuku daya, kowannensu na rike da wuka, suna sukan junan su. Suna  gaya wa juna “kai la’anance! A dalilin ka ne na zo nan! Ka sa ni na zo nan domin ka ki ka nuna mani gaskiya, ba ka bar ni in gane shi ba! Ba ka bar ni in karbe shi ba! Na sami zarafi dayawa amma ba ka bar ni in karbe shi ba! Shi ya sa ina nan, ina shan azaba dare da rana.”

Ta wahayi Ubangiji Ya nuna mana rayuwan su a duniya. Mun gan su a mashaya tare. Gardama  ya tashi har ya sa aka fara fada. Sun rigaya sun bugu da giya. Dayan su ya dauki fasasshen kwalba, dayan kuma wuka. Sun yi ta fada har sa’anda dukan su suka ji ciwo soasai har sun mutu. An kadara wa mutanen nan biyu suyi ta sake fadan su har abada. Wani abin azaba masu kuma shi ne tunanin cewa a duniya su abokanai ne soasai, kaunar su wa juna kamar na ‘yan uwa.

Ina so in gaya maku yau cewa, aboki daya ne kadai na gaskiya, sunansa Yesu banazare. Shi aboki ne na kwarai, ba zai taba yashe ka ba, yana nan tare da kai a kodayaushe.

Da muka cigaba tafiya, muka ga wata mace a cikin wata dakin kurkuku, ta na birgima a cikin laka. Sumar ta ya baci, a cike da laka. A cikin wannan dakin kurkukun akwai wani babban maciji mai kiba. Macijin  ya gusa kusa da ita, ya kewaye ta, sai ya shiga jikin ta, farawa daga kasan jikin ta. An tilasta ma ta yi zina da macijin. A wannan wajen, duk maza da matan da suka yi rayuwar zina, ana tilasta masu su yi ta yi anan. Amma kuma da macizai wadda suke da abubuwa masu tsini mai tsawon inchi shida a jikin su ne za su yi zinan. Duk sa’anda ya shiga, macijin sai ya rugurguza jikin ta. Ta yi kuka ga Ubangiji, ta roke Shi Ya sa macijin ya daina. Ba ta so ta wahala kuma:“Ka sa shi ya daina! Ba zan sake yi ba! Ka taimake ni! Ka sa shi ya daina!” tana rokon Ubangiji yayinda macijin yana ta shiga ya rugurguza jikin ta akai da kai.

Mun yi kokari mu rufe kunuwan mu daga kukan ta amma mun cigaba jin kukan. Mun kara kokari kuma mu rufe kunuwan mu amma bai hana mu ji ba. Sai muka cewa Ubangiji “Ka taimake mu, ba mu so mu ji wannan kuma!” Ubangiji ya ce, “ya kamata ku gani don ku gayawa sauran domin mutane na na hallaka, suna kin hanyar ceto, hanyan gaskiya na ceto”

Mun cigaba da tafiya sai muka ga wata katuwar tafki da duban mutane a tsakiyan harshen wuta. Suna daga hannuwan su suna rokon taimako, amma akwai aljannu dayawa da suke yawo a saman wurin.  Aljannun na amfani da mashin su suna yi wa mutanen rauni. Aljannun suna ta yi masu ba’a, suna kuma zagin su cewa “ku la’anannu! Yanzu dole ne ku bauta wa shaidan! Ku daukaka shi kamar yadda ku ke yi a duniya!” Akwai duban mutane a wurin nan. Mun razana sosai, muna ganin cewa idan ba mu rike hannun Ubangiji ba za a bar mu a wannan mummunar wajen. Mun tsorata kwarai da abubuwan da muke ji.

Daga nesa mun hangi wani mutum a tsaye, yana cikin wahala da radadi. Yana da aljannu guda biyu da suke yawo a kansa, suna ba shi azaba. Sai su shigar da mashin su cikin jikin sa su ciro hakarkarinsa. Suna ta yi masa ba’a. Banda haka, Ubangiji Ya nuna mani cewa abinda ya fi ba shi azaba shi ne damuwa akan iyalin sa da ya bari a duniya. Bayya son iyalin sa su zo wannan wuri mai wahala. Ya damu domin bai yi masu wa’azin ceto ba. Yana shan azaba domin ya tuna, a da suna da zarafi amma ya hana su karban ceto. Shi ne mutum mafi muhimmanci da zai bada wannan bishara amma ya kyalle, yanzu ya damu da ‘ya’yan sa da matar sa.

Azabar ta cigaba, aljannun suka cire hannayen sa sai suka bar shi ya fadi cikin laka mai konewa. Domin zafin lakar, yayi ta juyawa kamar tsutsa daga wuri daya zuwa wani. Namar sa suka fadi daga kasusuwan sa domin zafi. Sai ya fara sululu kamar maciji, yana kokarin ya fita amma duk lokacin da ya gwada, aljanun sai su tura shi ya koma cikin lakar.

Sai muka ga wasu a wani waje, wani abu ya dauki hankalin su, na gane cewa daya daga cikin aljanu ba yi da daya daga cikin fukafukinsa. Na tambayi Ubangjji “Ubangiji, me ya sa wannan aljannin bayi da fukafuki daya?” Ubangiji ya ce “wancan aljannin an tura shi duniya domin dalili daya amma bai iya yin aikin sa ba, sai wani bawan Allah ya turo shi jahannama. Sai kuma shaidan ya hore shi, ya yanke fukafukin sa daya.” Sai muka fahimci cewa, mu krista muna da iko cikin sunan Yesu mu cire aljannu da ikoki.

Abokannai na da ke sauraro yanzu, wannan shaida ba domin hallakar wa bane domin ceto ne, sai ka gwada kanka, ka san yanayin zuciyar ka a gaban Ubangiji. Wannan fa domin ka canja hanyoyin ka, don ceto ba domin hallaka ba ne. Yanzu, ka mika zuciyar ka ga Ubangiji ka kuma furta zunuban ka domin idan Ubangiji ya zo yanzu ka tafi tare da shi, ko kuma ka je wurin da akwai azaba, da kuka da cizon hakora. A wurin za ka gane dalilin da Yesu ya biya babban farashi akan giciye.

Mun ga mutane dayawa a jahannama wadda basu san dalilin da ya sa suke wurin ba. Rayuwar su na cike da ayyukan da ba su zata zunubi ba ne. Aboki na ka gwada kanka! Kar ka ga kamar karya, sata, girman kai abu mai kyau ne a yi! Duk wadannan zunubai ne a gaban Ubangiji! ‘Yan uwa, ku juya ku daina yin waddanan abubuwa! Ina ba ku wannan galgadin domin ku da kanku ku daina zunubi, sannan ku dubi fuskar Ubangiji.

 

......(Shaida ta shida).....

Zabura 62:12 “Madawwamiyar kauna, ta Ubangiji ce, kai kanka, ya Ubangiji, kake saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa”.

Wata safiya Ubangiji ya ziyarce mu a daki, ya rike hannun mu sai muka fara tafiya kasa. Zuciyata ta cika da tsoro, bazan iya kwatantawaba. Abin da na sani shine hannuna bazai rabu da na mai ceto ba. Na ji cewa Yesu ne rayuwata, da haske na, da kuma bege na, idan ba hakaba da an barni a wannan waje. Ban taba yin tunanin cewa zan je wancan waje ba, ban gaskanta cewa akwai wani wuri haka ba. Ni Krista ma na zata wajen da mutane zasu je a canja su shine jahannama amma Allah Ya nuna mani gaskiyan jahannama  

Da muka isa jahannama, na ji wurin ya girgiza. Duk aljannun suka gudu suka buya domin ba dayan su da zai iya tsayawa a gaban Ubangiji. Mun ji kukan rayukan da aka kama, domin Yesu banazare na wurin. Sun sani cewa mutum daya ne zai iya fitar da su, suna wannan bege kodashike ba begen gaskiya ba ne.

Mun yi tafiya hannu da hannu da Yesu har muka isa sashen zina. Yesu ya juya ya dubi wata mace wanda take rufe da wuta. Da Yesu ya kalli ta sai ta fara fita daga wutan da hankali kodashike wahalar ta bai tsaya ba. Mun ga tsirara ta ke, mun ga duk halayenta, jikin ta na da datti, tana wari, suman ta ya baci, tana da koren laka a jikin ta. Ba ta da idanu, leben ta ma na fadiwa. Ba ta da kunne sai ramumukan. Da hannun ta wanda duk kasusuwa ne tana kokarin maida naman fuskanta da ya fadi, amma zafi ne wannan ke kara ma ta.

Sai ta girgiza ta yi ihu sosai, ihun ta baya karewa, tana cike da tsutsotsi, akwai maciji a zagaye da hannun ta. Macijin na da kauri, yana da kuma kaya a jikin sa. Tana da lambar 666 wanda an kwarzana a jikin ta. Lambar nan ne da aka yi magana a Littafin Ruya ta Yohanna (Ruya ta Yohanna 13:16-18) tana da farantin karfe a kirjin ta wadda baya konewa da wuta. A kan farantin an rubuta wani abu da wata yare, amma mun fahinmci abinda aka rubuta. Yace: “Ina nan saboda zina”.

Da Yesu ya gan ta  ya tambaye ta “Elena me ya sa ki ke nan?” da Elena take amsa Yesu sai jikin ta yana ta juya domin azabar ta. Ta ce ita mai zina ce sau dayawa kuma ta yi ta rokon Ubangiji ya gafarta mata.

Sai mu ka fara ganin yadda ta mutu. Ta mutu tana zina da wani masoyin ta ne domin ta dauka cewa wanda take zama da shi yayi tafiya amma ya dawo daga aiki ya same ta a gado da wani.Sai ya je madafi ya dauko wuka ya soka a bayan Elena.Ta mutu an kai ta jahannama daidai yadda ta mutu; wato tsirara.

A jahannama kome ta dawo, tana da wukar a soke a bayan ta, yana sa mata ciwo mai zafi. A wannan lokaci ta yi shekaru bakwai (7) a jahannama ta tuna da duk rayuwarta da mutuwar. Ta tuna da lokacin da wani ya so yayi mata wa azi game da Yesu; cewa shine kadai zai ceceta amma yan zu yayi mata latti, da kuma sauran mutanen dake jahannama.

Maganar Ubangiji yayi magana a kan zina. Zina shine lalata a cikin aure. 1 Korantiyawa 6:13: “Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci – Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.”  Haka kuma a 1 Korantiyawa 6:18: “Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana daukar alhalin jikinsa ne.”

Da Yesu ya gama magana da ita, an rufe ta da babban bargon wuta, bamu iya ganinta ba kuma amma muna jin karan naman ta yana konewa da kururuwarta, bazan iya kwatantawa ba.

Da muka cigaba tafiya da Ubangiji, Ya nuna mana dukan mutane da ke wurin: da masu bautar gumaka, da masu maita, da masu fasikanci, da masu karya, da  masu luwadi. Mun tsorata, abu daya da muke so shi ne mu bar wannan wurin. Amma Yesu Ya yi ta cewa ya kamata ku kalla domin ku gaya wa wasu don su gaskanta.

Mun cigaba da tafiya da Yesu, muna rike da hannun sa sosai. Mun isa wani sashe da ya kayartar da ni. Mun ga wani saurayi mai shekaru ashirin da uku(23), yana soke daga kunkumin sa a tsakiyar wuta. Ba mu ga azabarsa ba amma mun ga lambar 666 a jikinsa. Yana da faranti na karfe a kirjinsa da aka rubuta “Ina nan domin zama yadda nake – rashin bagaskiya”. Da ya ga Yesu, ya mika hannunsa wurin Yesu yana rokon jinkai. Maganar Allah ya ce a Misalai 14:12, “Hanyar da kake tsammani ita ce daiadai, za ta kai ka ga hallaka.”

Da muka karanta farantin da ya ce, “ina nan domin zama yadda na ke”, mun tambayi Ubangiji “Ubangiji yaya ya faru? Yaya mutum zai zo nan domin wannan dalilin?” Yesu ya tambaye shi, “Andrew, me ya sa kake nan?” ya amsa, “Yesu, da nake duniya, na zata kisa da sata sune zunubi, shi ya sa ban nemi in yi kusa da kai ba”.  Zabura 9:17 ya ce “Mutuwa ce makarar dukan mugaye, da dukan wadanda suke kin Allah”

Falling into HellAndrew ya yi babbar kuskure da ya kassa zunubi, kamar mutane dayawa a yau. Littafi Mai Tsarki ya fada dalla-dalla cewa sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawammi (Romawa 6:23). Bugu da kari, Littafi Mai tsarki tayi magana a kan zunubi amma bata kasa zunubi ba domin dukansu zunubi ne. Andrew yana da zarafin sanin da kuma karban Ubangiji amma bai yi amfani da daman da Allah ya bashi ba. Sai babban bargo na wuta ya rufe jikinsa, bamu sake ganinsa ba.

Mun chigaba tafiya da Yesu, daga nesa munga wani abu na fadowa kamar gutsirin yadi, da muka matso kusa sai muka ga mutane ne suke fadowa zuwa jahannama. Wannan mutane sun mutu a duniya basu karbi Yesu Kristi cikin zuciyarsu ba, suna isowa jahannama kenan.

Munga wani saurayi, aljannu dayawa sun gudu zuwa wajen shi suna hallaka jikinsa. Nan da nan jikinsa ta fara cika da tsutsotsi. Yana ta ihu “A’a! Menene wannan? Ku daina! Bana son wannan wuri! Ku daina! Wannan mafalkine! Dauke ni daga nan!”Bai ma sani cewa mutuwa yayi ba, kuma ya mutu ba tare da Yesu a zuciyarsa ba. Aljannun suna ta dariyan sa, suna ta yi wa jikinsa azaba. Sai lambar 666 ta bayana a goshinsa, farantin karfe kuma a kirjinsa. Koda bamu san dalilin da ya sa ya zo jahannama ba, mun sani cewa bazai taba fitaba.

Ubangiji ya ce mana azabar mutane a jahannama zai karu a lokacin shari’a. Na gagara kwatanta azabar su a lokacin shari’a ganin wanda suke ciki yanzu.

Bamu ga yara a wajen ba amma munga dubai-dubai mutane; maza da mata daga kasashe dabam-dabam. Ko dashike a jahannama babu bambancin kasa ko matsayi dukansu sun zo domin su karbi azaba ne. Akwai abu daya da kowa yake so, wannan shine zarafi na biyu domin tuba. Suna so digon ruwa ya jika harshensu kamar a labarin mai arziki a cikin Littafi Mai tsarki (Luka 6:19). Amma ba zai yiwu ba kuma, sun zabi inda suke so su karasa rayuwarsu har’abada. Sun zaba suyi shi ba tare da Allah ba. Allah bayi da niyar tura wani jahannama, kowa yana zuwa ta dalilin ayukansa ne. A Galatiiyawa 6:7,“ kada fa a yaudare ku, a’a,ba a iya zambartar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba

Yau, kana da babban zarafin canja kaddararka. Yesu na nan a yalwace, kuma Littafi Mai-tsarki tace idan muna da rai muna da bege. Yau, kana  da rai, kar ka bari wannan zarafi ya wuce ka, mai yuwa, na karshen kane.

Allah ya albarkace ku…..