Zabura 54
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil* Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”
1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;
ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
2 Ka ji addu’ata, ya Allah;
ka saurari maganar bakina.
3 Baƙi suna kawo mini hari;
mutane marasa imani suna neman raina,
mutanen da ba sa tsoron Allah.
Sela
4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona,
Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;
cikin amincinka ka hallaka su.
6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;
zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,
idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.