Zabura 13
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne?
Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?
2 Har yaushe zan yi kokawa da tunanina
kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata?
Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?
3 Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.
Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;
4 abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,”
kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.
5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;
zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
6 Zan rera ga Ubangiji
gama ya yi mini alheri.