2
Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa. Ya ce,
“A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji,
ya kuwa amsa mini.
Daga cikin zurfi kabari* Sheol na Ibraniyanci na yi kiran neman taimako,
ka kuwa saurari kukata.
Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku,
ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa;
dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka
sun bi ta kaina.
Sai na ce, ‘An kore ni
daga fuskarka;
duk da haka zan sāke duba
wajen haikalinka mai tsarki.’
Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, Ko kuwa ruwaye sun kai ga maƙoshina
zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.
Na nutsa har ƙarƙashin tuddai;
a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada.
Amma ka dawo da raina daga rami,
Ya Ubangiji Allahna.
 
“Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni,
na tuna da kai ya Ubangiji,
addu’ata kuma ta kai gare ka,
a haikalinka mai tsarki.
 
“Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani,
sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.
Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
10 Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.

*2:2 Sheol na Ibraniyanci

2:5 Ko kuwa ruwaye sun kai ga maƙoshina