27
Bagade a kan Dutsen Ebal
1 Musa tare da dattawan Isra’ila suka umarci mutane suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai da na ba ku a yau. 2 Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa. 3 Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari. 4 Sa’ad da kuma kuka haye Urdun, ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal, kamar yadda na umarce a yau, ku yi musu shafe da farar ƙasa. 5 Ku gina bagade wa Ubangiji Allahnku, bagaden dutse. Kada ku yi amfani da wani kayan aiki na ƙarfe a kansu. 6 Ku gina bagaden Ubangiji Allahnku da duwatsun fili, ku kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kansa ga Ubangiji Allahnku. 7 Ku miƙa hadayun salama a can, kuna ci, kuna farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku. 8 Za ku kuma rubuta a fayyace dukan kalmomin wannan doka a kan waɗannan duwatsun da kuka kakkafa.”
La’anu daga Dutsen Ebal
9 Sai Musa da firistoci waɗanda suke Lawiyawa suka ce wa dukan Isra’ila, “Ku yi shiru, ya Isra’ila, ku saurara! Yanzu kun zama mutanen Ubangiji Allahnku. 10 Ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, ku bi umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau.”
11 A wannan rana Musa ya umarce mutane,
12 Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin. 13 Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.
14 Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,
15 “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
16 “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
17 “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
18 “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
19 “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
20 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
21 “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
22 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
23 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
24 “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
25 “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
26 “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”