Zabura 101
Ta Dawuda. Zabura ce. 
 1 Zan rera wa ƙauna da adalcinka; 
gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo. 
 2 Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, 
yaushe za ka zo gare ni? 
Zan bi da sha’anin gidana 
da zuciya marar abin zargi 
 3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1 
wani abu marar kyau ba. 
Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; 
ba za su manne mini ba. 
 4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; 
ba abin da zai haɗa ni da mugunta. 
 5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye 
shi za a kashe; 
duk mai renin wayo da mai girman kai, 
ba zan jure masa ba. 
 6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, 
don su zauna tare da ni; 
tafiyarsa ba ta da zargi 
zai yi mini hidima. 
 7 Babu mai ruɗun 
da zai zauna a gidana; 
babu mai ƙaryan 
da zai tsaya a gabana. 
 8 Kowace safiya zan rufe bakunan 
dukan mugaye a ƙasar; 
zan yanke kowane mai aikata mugunta 
daga birnin Ubangiji.