Zabura 24
Zabura ta Dawuda. 
 1 Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, 
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; 
 2 gama ya gina ta a kan tekuna 
ya kafa ta a kan ruwaye. 
 3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? 
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki? 
 4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, 
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki 
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya. 
 5 Zai sami albarka daga Ubangiji 
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa. 
 6 Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, 
waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. 
Sela
  7 Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; 
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, 
don Sarkin ɗaukaka yă shiga. 
 8 Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? 
Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, 
Ubangiji mai girma a yaƙi. 
 9 Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; 
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, 
don Sarkin ɗaukaka yă shiga. 
 10 Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? 
Ubangiji Maɗaukaki, 
shi ne Sarkin ɗaukaka. 
Sela