20
1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;
duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
2 Fushin sarki yana kama da rurin zaki;
duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
3 Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,
amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
4 Rago ba ya noma a lokacin noma;
saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
5 Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne,
amma mutum mai basira yakan jawo su.
6 Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne,
amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
7 Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
8 Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a,
yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
9 Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki;
ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
10 Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba,
Ubangiji ya ƙi su duka.
11 Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,
ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
12 Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani,
Ubangiji ne ya yi su duka.
13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;
ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
14 “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya;
sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
15 Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace,
amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
16 A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo;
a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
17 Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi,
amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
18 Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara;
in kana yaƙi, ka sami bishewa.
19 Mai gulma yakan lalace yarda;
saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
20 In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,
fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
21 Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa
ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
22 Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!”
Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
23 Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba,
da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
24 Ubangiji ne yake bi da matakan mutum,
Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
25 Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani
daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
26 Sarki mai hikima yakan gane mugunta;
ya hukunta su ba tausayi.
27 Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum
takan bincika lamirinsa.
28 Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya;
ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
29 Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu,
furfura ita ce darajar tsofaffi.
30 Naushi da rauni kan share mugunta,
dūka kuma kan tsabtacce lamiri.