Karin maganar Solomon
10
1 Karin maganar Solomon.
Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2 Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka,
amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
3 Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa
amma yakan lalace burin mugu.
4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,
amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,
amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
6 Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani,
amma rikici kan sha bakin mugu.
7 Tunawa da mai adalci albarka ne
amma sunan mugu zai ruɓe.
8 Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni
amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
9 Mai mutunci yana tafiya lafiya,
amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
10 Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki
surutun wawa kuma kan zo da lalaci.
11 Bakin adali maɓulɓulan rai ne,
amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12 Ƙiyayya kan haddasa wahala,
amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
13 Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi,
amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
14 Mai hikima kan yi ajiyar sani,
amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
15 Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu,
amma talauci shi ne lalacin matalauci.
16 Hakkin adalai kan kawo musu rai,
amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci.
17 Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai,
amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.
18 Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa,
duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.
19 Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki,
amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.
20 Harshen adali azurfa ce zalla,
amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.
21 Leɓunan adalai kan amfane yawanci,
amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.
22 Albarkar Ubangiji kan kawo wadata,
ba ya kuma ƙara wahala a kai.
23 Wawa yakan ji daɗi halin mugunta,
amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.
24 Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi;
abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.
25 Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye,
amma adalai za su tsaya daram har abada.
26 Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu,
haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
27 Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai,
amma akan gajartar da shekarun mugaye.
28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki,
amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
29 Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai
amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
30 Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba,
amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba.
31 Bakin adalai kan fitar da hikima,
amma za a dakatar da mugun harshe.
32 Leɓunan adalai sun san abin da ya dace,
amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai.