19
Ayuba
1 Sai Ayuba ya amsa,
2 “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba
ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
3 Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni,
kuna kai mini hari na rashin kunya.
4 In gaskiya ne na yi laifi,
kuskurena ya rage nawa.
5 In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina
kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,
6 sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba
ya kewaye ni da ragarsa.
7 “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba;
ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.
8 Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba;
ya rufe hanyata da duhu.
9 Ya cire darajar da nake da ita,
ya kuma cire rawani daga kaina.
10 Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare;
ya tuge begen da nake da shi kamar itace.
11 Yana jin haushina
ya lissafta ni cikin maƙiyansa.
12 Rundunarsa ta zo da ƙarfi;
suka kafa sansani kewaye da ni,
suka zagaye tentina.
13 “Ya raba ni da ’yan’uwana maza;
abokaina sun zama baƙi gare ni.
14 Dangina sun tafi;
abokaina na kurkusa sun manta da ni.
15 Waɗanda sukan ziyarce ni,
da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.
16 Na kira bawana, amma bai amsa ba,
ko da yake na roƙe shi da bakina.
17 Numfashina yana ɓata wa matata rai;
’yan’uwana sun ƙi ni.
18 Har ’yan yara suna rena ni;
in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
19 Duk abokaina sun yashe ni;
waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
20 Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi,
da ƙyar na tsira.
21 “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina,
gama hannun Allah ya sauko a kaina.
22 Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi?
Ba ku gaji da yagar fatata ba?
23 “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna,
da an rubuta su a littafi,
24 a rubuta su da ƙarfe a kan dutse
don su dawwama har abada!
25 Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,
kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
26 Kuma bayan an hallaka fatata,
duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
27 Zan gan shi da kaina
da idanuna, Ni, ba wani ba ne.
Zuciyata ta cika da wannan tunani!
28 “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini,
tun da shi ne tushen damuwa,’
29 sai ku ma ku ji tsoron takobin;
gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi,
sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”