23
Reshen adalci
1 “Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji. 2 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji. 3 “Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya. 4 Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.
5 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan tā da wa Dawuda* Ko kuwa tā da daga zuriyar Dawuda Reshen adalci,
Sarki wanda zai yi mulki da hikima
ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
6 A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda
Isra’ila kuma zai zauna lafiya.
Sunan da za a kira shi ke nan,
Ubangiji Adalcinmu.
7 “Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’ 8 amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.”
Annabawa masu ƙarya
9 Game da annabawa kuwa,
Zuciyata ta karai;
dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa.
Na zama kamar wanda ya bugu,
kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa,
saboda Ubangiji
da kuma maganarsa mai tsarki.
10 Ƙasar ta cika da mazinata;
saboda la’ana† Ko kuwa saboda waɗannan abubuwa ƙasar ta zama kango‡ Ko kuwa ƙasar yana kuka
makiyaya a hamada ta bushe.
Annabawa suna bin mugayen muradu
suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau.
11 “Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne;
har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,”
in ji Ubangiji.
12 “Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi;
za a jefar da su cikin duhu
a can kuwa za su fāɗi.
Zan kawo musu masifa
a shekarar da za a hukunta su,”
in ji Ubangiji.
13 “A cikin annabawan Samariya
na ga wannan abin banƙyama.
Suna annabci ta wurin Ba’al
suna ɓad da mutanena Isra’ila.
14 A cikin annabawan Urushalima kuma
na ga wani abin bantsoro.
Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya.
Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta,
domin kada wani ya juya daga muguntarsa.
Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni;
mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”
15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa,
“Zan sa su ci abinci mai ɗaci
su kuma sha ruwa mai dafi,
domin daga annabawan Urushalima
rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”
16 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci;
suna cika ku da sa zuciyar ƙarya.
Suna maganar wahayi daga tunaninsu,
ba daga bakin Ubangiji ba.
17 Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni,
‘Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’
Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa
sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’
18 Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji
yă ga ko ya ji maganarsa?
Wa ya saurari ya kuma ji maganarsa?
19 Ga shi, hadarin Ubangiji
zai taso cikin hasala
guguwa tana kaɗawa
a kan kawunan mugaye.
20 Fushin Ubangiji ba zai kau ba
sai ya aikata
nufin zuciyarsa.
A kwanakin masu zuwa
za ku gane sarai.
21 Ban aiki waɗannan annabawa ba,
duk da haka sun tafi da saƙonsu;
ban yi musu magana ba,
duk da haka sun yi annabci.
22 Amma da a ce sun tsaya a majalisata,
da sun yi shelar maganata ga mutanena
sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu
da kuma daga mugayen ayyukansu.
23 “Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,”
in ji Ubangiji,
“ba Allah na nesa ba?
24 Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?”
In ji Ubangiji
“Ban cika sama da ƙasa ba?”
In ji Ubangiji.
25 “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ 26 Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? 27 Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. 28 Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji. 29 “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?
30 “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna. 31 I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’ 32 Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
33 “Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganar§ Ko kuwa nawaya (dubi Seftuwajin da Bulget)Ubangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana?* Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Bulget Ku ne nawayar. (Ibraniyanci na faɗar Ubangiji da nawaya sun yi kama da juna.) Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’ 34 In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa. 35 Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ 36 Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu. 37 Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ 38 Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’ 39 Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku. 40 Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”