15
Abiya sarkin Yahuda
(2 Tarihi 13.1-22)
1 A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda, 2 ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom.
3 Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba. 4 Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi. 5 Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti.
6 Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya. 7 Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam. 8 Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
Asa sarkin Yahuda
(2 Tarihi 15.16–16.6,11-13)
9 A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda, 10 ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom.
11 Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. 12 Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi. 13 Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. 14 Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa. 15 Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji.
16 Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. 17 Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
18 Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. 19 Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
20 Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali. 21 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza. 22 Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.
23 Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta. 24 Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Nadab sarkin Isra’ila
25 Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu. 26 Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
27 Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto. 28 Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki.
29 Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo. 30 Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi.
31 Game da sauran ayyukan mulkin Nadab da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 32 Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
Ba’asha sarkin Isra’ila
33 A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu. 34 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.